Hukumar zaben mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta ce za ta yi amfani da na’urar mazu zabe ta Card Reader kamar yadda aka yi a zabubbukan shekara ta 2015.
Mai magana da yawun hukumar Mallam Aliyu Bello, ya ce ganin yadda na’urar ta taimaka wajen gudanar da sahihin zabe a shekara ta 2015, ya sa a yanzu ma za a yi amfani da ita.
Sai dai hukumar ta ce ba za a yi amfani da na’urar ba wajen aikewa da sakamakon zaben shugaban kasa daga jihohi zuwa hedikwatarta dake Abuja ba, sai dai a kai shi a takarda.
Hukumar zaben dai ta bayyana haka ne, makonni kadan bayan shugabaMuhammadu Buhari ya yi watsi da dokar da majalisar dokoki ta tarayya ta amince da ita, wadda ta nemi a wajabta wa hukumar amfani da na’urar a dukkan tsarin zabubbuka.
Mallam Aliyu Bello, ya ce a cikin shirye-shiryen da hukumar ke yi don ganin an yi sahihin zabe, ta kara inganta sauri da kuma nagartar na’urar yadda ba za a samu wata matsala ba.

Zaben 2019: Za Mu Yi Amfani Da Na’urar Card Reader - Inec newspaper mockup | |
1 Likes | 1 Dislikes |
39 views views | 8.43K followers |
News & Politics | Upload TimePublished on 11 Jan 2019 |
No comments:
Post a Comment